Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane 330,000 ne suka fita daga kangin talauci a yankin arewa maso gabashin kasar Sin
2019-11-18 12:14:05        cri

Hukumar yaki da talauci ta lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin, ta ce jimilar mutane 334,000 na lardin ne suka yi adabo da talauci tun daga shekarar 2017.

Ya zuwa watan Yulin bana, kaso 0.65 na jimilar al'ummar yankin ne kadai ke cikin talauci.

Cikin sama da shekaru 2 da suka gabata, kauyuka 1678 daga cikin 1778 na lardin Heilongjiang ne suka yi ban kwana da talauci.

Dukkan kauyuka na da ingantattun hanyoyin sufuri da sadarwar intanet da na shirye shiryen talabijin da asibitoci da kuma cibiyoyin gudanar da harkokin al'adu.

Kasar Sin na da burin fatattakar talauci baki daya ya zuwa shekarar 2020, wadda ta kasance shekarar da aka sanya na cimma samun al'umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne bangare. Yayin da lokacin ke karatowa, kasar Sin ta rubanya kokarinta na mayar da hankali kan mutane mafi talauci dake kauyuka bisa amfani da matakai na musammam. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China