Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron yaki da talauci na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2019
2019-10-16 20:00:04        cri

Ran 17 ga wata, ita ce ranar yaki da talauci ta kasar Sin, kuma ranar kawar da kangin talauci ta duniya. Yau Laraba, an gudanar da taron yaki da talauci na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2019 a nan birnin Beijing, mai taken "More dabarar kawar da kangin talauci don gaggauta ayyukan yaki da talauci a duniya". Wakilai fiye da 200 daga kungiyoyin kasa da kasa 13 da kasashe 30 sun halarci taron, inda suka yi tattaunawa mai zurfi kan abubuwan da za a koya a aikin kawar da talauci da Sin take gudanarwa da manufofin da Sin ta gabatar wajen kawar da yunwa da talauci a duniya baki daya, matakin da ya taimakawa duniya a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China