Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana sa ran tsame mutane miliyan 10 daga kangin talauci a 2019
2019-12-16 10:16:17        cri

Wani jami'in gwamnatin Sin ya ce kasar tana sa ran tsame mutane sama da miliyan 10 daga kangin fatara ya zuwa karshen shekarar 2019.

Sama da kashi 95 bisa 100 na matalautan kasar Sin ake sa ran tsamewa daga talaucin, kana sama da yankuna 90 mafiya fama da karancin wadata ake fatan fitarwa daga kangin fatara ya zuwa karshen wannan shekarar, a cewar Liu Yongfu, daraktan ofishin shirin yaki da fatara na majalisar gudanarar kasar Sin.

Liu ya fada yayin taron kungiyar ma'aikatan sa kai masu rajin yaki da fatara na kasar Sin cewa, gwamnatin Sin za ta yi iyakar kokarinta na ganin ta cimma nasarar aiwatar da cikakken shirinta na yaki da fatara a shekara mai zuwa.

A matakai na gaba, Liu ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar da shirin yaki da fatara a yankunan dake fama da matsanancin talauci kuma za ta tattara manyan nasarorin da ta samu game da shirin yaki da fatara.

Da yake yin kira ga kungiyoyin al'umma, Liu ya ce, aikin yaki da fatara ba hakki ne da ya rataya kan gwamnati ita kadai ba, sai dai hakki ne dake kan dukkan al'umma.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China