Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kaddamar da shirin tallafawa matalauta na wucin gadi
2019-10-25 10:44:32        cri

Ma'aikatar kyautata jin dadin jama'a ta kasar Sin (MCA) ta bullo da shirin bada tallafi na wucin gadi don warware matsalolin kangin talauci, shirin zai samar da tallafi na muhimman bukatun al'umma kana zai kasance a matsayin hanyar riga kafin hana mutane sake fadawa cikin kangin talauci.

Shirin na hadin gwiwa ne tsakanin MCA, da ma'aikatar kudi, da kuma babban ofishin hukumar yaki da fatara na majalisar gudanarwar kasar Sin, shirin bada tallafin ya kunshi samar da abinci, tufafi, ilmi, kula da lafiya, da samar da ingantaccen muhallin zama ga mutane marasa sukuni, a cewar Liu Xitang, jami'in ma'aikatar jin da dadin jama'a ta kasar Sin MCA.

Shirin tallafin na wucin gadi zai shafi iyalai da suka fada cikin halin fatara ne a sakamakon afkuwar ibtila'in cutuka, ko kauracewa matsugunansu, da sake gina wuraren da bala'i ya shafa da kuma ilmin yara kanana.

Shirin zai kuma dinga bibiyar iyalan da suka riga suka kubuta daga kangin talauci kana zai dinga ba su taimako daga lokaci zuwa lokaci domin hana su sake fadawa cikin yanayin talaucin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China