Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta samu gagarumar nasara a yaki da talauci
2020-01-15 10:10:06        cri
Abhijit Banerjee, Ba'Amurke, masanin harkokin tattalin arziki, ya ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen yaki da talauci, cikin shekaru 20 da suka gabata.

Yayin bude taro kan harkokin kudi na nahiyar Asiya karo na 13 a birnin Hong Kong, wanda ya gudana ranar Litinin da Talata, Abhijit Banerjee, wanda kuma ya taba samun lambar yabo ta Nobel, ya yabawa kokarin kasar Sin na fitar da mutane daga kangin talauci. Yana mai cewa, al'ummar Sinawa na kokarin rayuwa a wani mataki mai inganci, wanda ke zaman sabon kalubale.

Tun bayan fara aiwatar da manufar bude kofa da gyare-gyare a gida, kasar Sin ta fitar da mutane sama da miliyan 800 daga kangin talauci, adadin da ya mamaye kaso 70 na yawan wadanda suka yi ban kwana da Talauci a duniya.

Abhijit Banerjee, wanda ya samu lambar Nobel tare da Farfesa Esther Duflo ta Jami'ar MIT da Farfesa Micheal Kremer na Jami'ar Harvard, saboda dabararsu ta kawar da talauci a duniya, ya ce, kasar Sin ta samu nasara a fannin rage talauci da cimma daidaito tsakanin al'ummarta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China