Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gama aikin yaki da talauci yadda ya kamata a 2020
2019-12-26 11:11:40        cri

Memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban rukunin kula da yaki da talauci da raya kasa na majalisar gudanarwar kasar Hu Chunhua ya yi bincike kan aikin yaki da talauci a lardin Hubei tun daga ranar 24 zuwa 25 ga wata, A yayin ziyararsa, Hu Chunhua ya jaddada cewa, ya kamata a koyi manufofin da shugaba Xi Jinping ya gabatar game da yaki da talauci, da aiwatar da tunanin taron ayyukan tattalin arzikin kasar, da daukar matakai bisa manufofin kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin don gama ayyukan da aka tsara da yaki da talauci yadda ya kamata.

Hu Chunhua ya jaddada cewa, aikin yaki da talauci shi ne aiki mafi muhimmanci na raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni, kuma tilas ne a gama aikin a shekarar badi. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China