Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin ladabtarwar Sin ya tsara aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa na shekarar 2020
2020-01-13 10:57:15        cri
Yau Litinin da safe, an bude cikakken zaman taron hukumomin bincike da sa ido na kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin na shekarar 2020, wato, cikakken zaman taron na hudu na kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiyar JKS karo na 19 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Yayin taron, za a tsara aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa da za a gudanar a sabuwar shekara ta 2020.

A shekarar 2019 da ta gabata, kasar Sin ta ci gaba da dukufa kan aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa. Kuma bisa kididdigar da kafofin watsa labaran kasar suka yi, an ce, daga watan Janairu zuwa watan Oktoba, gaba daya an kama wadanda suka aikata laifin cin hanci da karbar rashawa suka gudu zuwa kasashen waje guda 1634, kudaden da aka kwato sun kai RMB miliyan 2954, adadin da ya karu matuka idan aka kwatanta da na shekarar 2018.

A shekarar 2020 kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata tsarin sa ido na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na gwamnatin kasar Sin, domin karfafa aikin bincike da sa ido kan masu rike da mukamai (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China