Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da babbar cibiyar taro ta kasa da kasa wanda Sin ta gina a Gambia
2020-01-12 16:25:51        cri
A ranar Asabar kasar Gambiya ta kaddamar da cibiyar taro ta kasa da kasa wanda kasar Sin ta gina a Gambiyan.

Cibiyar mai fadin mita 14,000, akwai babban dakin taro mai daukar mutane 1,000, da dakunan taro hudu masu daukar mutane 200, da cibiyoyin 'yan jaridu kimanin 4, da wasu dakunan ganawa kimanin 14, da bangaren ofisoshi, da wuraren cin abinci, da sauran muhimman dakuna duk na kunshi cikin katafaren ginin cibiyar.

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya ce, wannan ita ce sabuwar kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa ta cin moriyar juna dake tsakanin Afrika da Sin.

Barrow ya bayyana cewa, yayi amanna cibiyar zata baiwa kasar Gambiya damammakin janyo hankali da karbar bakuncin muhimman taruka da masu yawon shakatawa, da kuma tarukan baje koli.

Ya kara da cewa, cibiyar zata samar da damammakin guraben aikin yi, kana zata bunkasa harkokin yawon shakatawa, da kyautata ayyukan sufuri, da tallata al'adun kasar Gambiya a idanun kasashen duniya.

A cewar ministan sufurin kasar Gambiyan, Bai Lamin Jobe, a kwanan baya an horas da 'yan asalin kasar Gambiya su 20 a kasar Sin game da yadda zasu tafiyar da ayyukan cibiyar, inda aka baiwa cibiyar sunan shugaban kasar Gambiya na farko Sir Dawda Kairaba Jawara.

Wannan shi ne aiki na farko da kasar Sin ta gudanar a kasar Gambiya tun bayan farfado da huldar dake tsakanin kasashen biyu a shekarar 2016.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China