Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya yi kira da a daga matsayin muhimmin kawancen Sin da Masar
2020-01-09 09:38:32        cri

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira da a dauki karin matakan daga matsayin hadin gwiwa daga dukkanin fannoni, dake tsakanin Sin da Masar zuwa wani sabon matsayi, domin cimma nasarar gina al'umma mai makoma guda a sabon zamanin da ake ciki.

Wang ya yi wannan tsokaci ne yayin ganawar sa da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, a fadar sa dake birnin Alkahiran kasar ta Masar. Ya ce a matsayin ta na dadaddiyar kawa kuma aminiya ga Masar, Sin za ta ci gaba da goyon bayan Masar din wajen samun cikakken ikon mulkin sassan ta, da bin hanyar ci gaba mafi dacewa da yanayin da kasar ke ciki, da dakile daukacin nau'ikan ayyukan ta'addanci, da tsattsauran ra'ayi.

A nasa tsokaci kuwa, shugaba Sisi ya jinjinawa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma da Sin ta samu, yana mai fatan dorewar cikakkiyar hulda daga dukkanin fannoni tsakanin kasar sa da Sin. A hannu guda kuma ya godewa Sin, bisa dadadden goyon baya da take baiwa Masar.

Shugaba Sisi ya ce, Masar na aiki tare da Sin, don cimma nasarar daga darajar dangantakar sassan biyu daga dukkanin fannoni zuwa mataki na gaba, da goyon baya ga shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya" wadda Sin ta gabatar. Ya ce Masar na fatan zama abokiyar hulda da za ta taimaka, wajen cimma nasarar wannan shawara da Sin ta gabatar.

Shugaban na Masar ya kuma ce a halin yanzu, kasar sa na kan wata gaba ta samun ci gaba da farfadowa, tana kuma fatan karfafa hadin gwiwar cin moriyar juna a fannoni daban daban tare da Sin, da kuma yin musayar dabarun yaki da ta'addanci, da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.

Daga nan sai shugaba Sisi ya jinjinawa matsayin Sin na rungumar adalci, a dukkanin al'amura da suka shafi kasa da kasa, yana mai burin ganin Sin din ta kara taka rawar gani, a kokarin da ake yi na dakile wutar tashin hankali dake ruruwa a gabas ta tsakiya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China