Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar da takardar bayani ta farko kan yadda za a hukunta masu cin zarafin 'yan sanda
2020-01-10 15:48:38        cri

Kwanan nan, kasar Sin ta fitar da takardar bayani ta farko kan yadda za a hukunta masu cin zarafin 'yan sanda bisa doka. Wannan ita ce takarda ta farko da aka fitar bisa hadin gwiwar kotun kolin jama'ar kasar Sin, da hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar, da kuma ma'aikatar tsaron lafiyar jama'ar kasar, musamman domin hukunta masu aikata manyan laifuffuka.

Jami'i mai kula da sassan da abin ya shafa a ma'aikatar tsaron lafiyar jama'ar Sin ya bayyana yau Jumma'a ranar 10 ga wata, cewar takardar ta yi bayanin cewa, yanayin da aka kaiwa 'yan sanda hari ko cin zarafin su, akwai yiwuwar yanke mummunan hukunta, lamarin da ya shaida muhimmancin da ake dorawa kan batun da ya shafi cin zarafin 'yan sanda. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China