![]() |
|
2020-01-09 16:01:20 cri |
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma Ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce Sin da Masar sun amince su bunkasa dangantakar dake tsakaninsu ta hanyar inganta hadin gwiwa a dukkan bangarori.
Wang Yi ya bayana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Masar, Sameh Shoukry, da ya gudana a birnin Cairo na Masar.
Bayan muhimmiyar tattaunawar da suka yi, Ministocin biyu sun cimma matsaya kan batutuwa da dama.
Har ila yau, Wang Yi ya ce, bangarorin biyu sun kuma amince su bunkasa dangantakarsu da nufin gina al'umma mai makoma ta bai daya a sabon zamani, yana mai cewa Kasar Sin ce babbar abokiyar huldar cinikayya ta Masar, inda jarin da ta zuba a kasar ya karu da kaso 60 a shekarar 2019. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China