Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dokokin Amurka ta zartar da kudirin dokar takawa Trump birki game da yaki da Iran
2020-01-10 10:55:45        cri

A ranar Alhamis majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da kudirin doka da nufin takawa shugaban kasar Donald Trump birki na hana shi yin amfani da karfin iko wajen daukar matakin soji kan kasar Iran ba tare da sahhalewar majalisar dokokin Amurka ba.

Kudirin dokar ya samu goyon bayan 'yan majalisar 224 yayin da mambobi 194 suka yi watsi da shi.

Kudirin dokar ya umarci shugaban kasar da ya janye aniyarsa ta yin amfani da jami'an sojojin Amurka wajen yin ramuwar gayya kan kasar Iran, har sai idan shugaban ya samu amincewar majalisar dokokin ko kuma sai idan ya zama babu makawa sai an yi amfani da matakin sojin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China