Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya yiwa Iran kashedi da kada ta yi yunkurin kaiwa Amurkawa hari don za ta maida martani
2020-01-05 16:13:56        cri
Jiya Asabar, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi gargadi ga kasar Iran cewa, idan ta kuskura ta kai hari ga dan kasar Amurka ko kuma kayayyakinta, nan da nan, Amurkar za ta maida martani gare ta kan muhimman abubuwa 52 na Iran.

A wannan rana, Trump ya sanar a shafinsa na Twitter cewa, kasar Amurka ta ki kowane irin kalubalen da aka yi mata, idan kasar Iran ta kai hari ga mutanen kasar Amurka ko kayayyakinta, kasar Amurka za ta maida martani mai tsanani kuma cikin sauri kan muhimman abubuwan kasar Iran.

Bisa labaran da aka samu daga kafofin watsa labaran kasar Amurka, an ce, dalilin da ya sa, kasar Amurka ta zabi abubuwan Iran guda 52 shi ne, domin maida martani ga kasar Iran kan rikicin Tehran, inda kasar Iran ta yi garkuwa da ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Amurka guda 52. Haka kuma, Donald Trump ya ce, wasu daga cikin wadannan abubuwa 52 suna da muhimmanci ga kasar Iran.

A ranar 3 ga wata, babban kwamandan rundunar sojan IRGC wato Qasem Soleimani ya rasu sakamakon harin makamai masu linzami da rundunar sojan kasar Amurka ta kai masa a lokacin da ayarin motocinsa suke gudu a kan wata hanyar dake kusa da babban filin saukar jiragen saman kasa da kasa dake birnin Bagadaza na kasar Iraki. Sa'an nan, jagoran kolin kasar Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya sanar da cewa, kasar Iran za ta maida martani mai tsanani kan wannan hari. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China