Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta kara tura sojoji kimanin dubu 3 zuwa yankin gabas ta tsakiya
2020-01-04 16:37:13        cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar a jiya, kasar ta shirya da kara tura sojoji kimanin dubu 3 zuwa yankin gabas ta tsakiya don tinkarar barazana a yankin.

Gidan rediyon NBC na kasar Amurka ya bayar da labarin cewa, jami'an ma'aikatar tsaron kasar da jami'an sojojin kasar sun tabbatar da cewa, za a kara tura sojoji kimanin dubu 3 zuwa yankin gabas ta tsakiya, wadanda za su zauna a yankin har na tsawon kwanaki kimanin 60. Bisa labarin da jaridar The Wall Street Journal ta tsamo daga maganganun jami'an kasar, an ce, wasu sojojin da aka kara turawa yankin za su isa kasar Kuwait a karshen wannan mako.

A wannan rana, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ya sanar da cewa, rukunin tinkarar yanayin ko-ta-kwana na rundunar sojojin sama ta 82 ta kasar suna cikin halin shirin yaki, an kuma jibge wani reshen rukunin a yankin gabas ta tsakiya, za kuma a jibge sauran rassan rukunin a kasar Kuwait.

An kai harin boma-bomai uku a filin jiragen sama na birnin Baghdad a kasar Iraki, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 8, ciki har da babban kwamandan rundunar sojan IRGC ta Iran wato Qasem Soleimani. A cikin wata sanarwar da ma'aikatar tsaron Amurka ta bayar, shugaban kasar Amurka Donald Trump ne ya bada umurnin kai hari kan Qasem Soleimani. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China