Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami kan sojojinta dake Iraqi
2020-01-08 10:45:07        cri

Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa, Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami sama da dozen a kan sojojinta da dakarun kawance dake Iraqi.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce da misalin karfe 5:30 na yamma jiya Talata, Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami sama da 12 kan dakarun Amurka da na kawancen kasashe.

Sanarwar ta ce a bayyane yake cewa, an kaddamar da hare-haren ne daga Iran, kuma aka auna su kan akalla sansanoni biyu na Al-Assad da Irbil, na sojojin Amurka da kawance kasashe.

Da farko a jiyan, Fadar White House ta ce ta samu rahotonnin hare-hare kan kadarorin kasar dake Iraqi, inda ta ce, shugaba Donald Trump na bibiyar yanayin, kuma yana tuntubar tawagarsa ta tsaron kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China