Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin sama da Amurka ta kai ga Soleimani ya keta dokar kasa da kasa, in ji Rasha
2020-01-05 16:39:21        cri
Jiya Asabar, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, ya yi hira da takwarorinsa na kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu da na kasar Iran Mohammad Javad Zarif ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa, harin da kasar Amurka ta kai a babban filin saukar jiragen saman kasa da kasa dake birnin Bagadaza na kasar Iraki, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar babban kwamandan rundunar sojan IRGC wato Qasem Soleimani ya keta babbar ka'idar dokar kasa da kasa kwarai da gaske.

Bisa labarin da shafin intanet na ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ya fidda, an ce, cikin hirar da ya yi da Mohammad Javad Zarif, Sergei Lavrov ya ce, harin sama da kasar Amurka ta kai ya keta ka'idar dokar kasa da kasa, zai kuma haddasa illa ga batun warware matsalar yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da zai kawo tabarbarewar yanayi a yankin.

Kana, cikin hirar da ya yi da Mevlut, Sergei Lavrov ya ce, matakin da kasar Amurka ta dauka zai haddasa illa ga shirin yaki da ta'addanci da gwamnatin kasar Amurka ke yi. Kasar Rasha da kasar Turkiya dukkansu sun nuna damuwa matuka dangane da mugun sakamako mai tsanani da kasar Amurka za ta kawowa yankin Gabas ta Tsakiya ta fuskar kiyaye zaman lafiya da zaman karko.

Da sanyin safiyar ranar 3 ga wata, babban kwamandan rundunar sojan IRGC wato Qasem Soleimani ya rasu sakamakon harin makaman roka da rundunar sojan kasar Amurka ta kai a hanyar dake kusa da babban filin saukar jiragen saman kasa da kasa dake birnin Bagadaza na kasar Iraki. Daga bisani kuma, hukumar tsaron kasar Amurka ta fidda wata sanarwa cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bada umurnin kai hari ga Qasem Soleimani. Sa'an nan, jagoran kolin kasar Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya sanar da cewa, kasar Iran za ta maida martani mai tsanani kan wannan hari. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China