Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 12 a harin wani kauye a tsakiyar Najeriya
2020-01-10 10:42:28        cri

Hukumar 'yan sanda a kasar Najeriya ta ce, an kashe mutane 12 da kuma raunata wani mutum guda a harin da 'yan bindiga suka kaddamar a wani kauye dake shiyyar tsakiyar Najeriya, da kuma kaddamar da ta'addanci kan mazauna yankin.

Kakakin 'yan sandan jahar Plateau Terna Tyopev, ya fadawa manema labarai cewa, kawo yanzu ba su kama wadanda ake zargi da kai harin na kauyen Kulben dake gundumar Kombun na karamar hukumar Mangu ta jahar Plateau ba.

Tyopev ya kara da cewa, tuni jami'an tsaron suka fara bincike game da harin, amma ba a gano hakikanin manufar maharan ba.

Wani mazaunin wurin ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ana zargi wasu makiyaya ne suka shiga kauyen, suka bude wuta kan mazauna kauyen.

Tyopev ya nuna cewa, tuni jami'an tsaro suka mamaye hanyar zuwa kauyen domin dakile karin wasu hare-haren. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China