Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayin dan jaridar NAN na Najeriya kan jawabin Shugaba Xi Jinping na murnar zuwan shekarar 2020
2020-01-01 15:58:36        cri
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta 2020 a jiya, 31 ga watan Disamban shekarar 2019.

Cikin jawabin, shugaba Xi ya yi bitar nasarorin da Sin ta samu cikin shekarar 2019, tare da fatan samun karin ci gaba a shekarar 2020.

Bayan da ya karanta jawabin, Lawal Sale, shugaban sashen hulda da jama'a na kamfanin dillancin labarai na Tarayyar Najeriya NAN, ya rubuto wa sashen Hausa na CRI wasika, domin bayyana ra'ayinsa kan jawabin. A cewar Lawal Sale, ya yi matukar sha'awar kalamomin shugaban, da kuma abubuwan ci gaba da kasar Sin ta samu ko kuma ta aiwatar a shekarar 2019. Ya lura cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa, har ma'unin GDPn ta ya kai kusan yuan triliyan 100, kana matsakaicin kudin shigar daidaikun al'ummar kasar zai kai dalar Amurka dubu 10, yana mai bayyana shi a matsayin babban nasara.

Ban da wannan kuma, Lawal Sale ya yi nuni cewa, wani abun sha'awa a cikin jawabin shi ne a fannin kere-kere da kirkire-kirkire, inda a shekarar 2019 kamar yadda shugaba Xi ya ce, Sin ta harba roka mai dakon kaya zuwa sararin samaniya, da kaddamar da jirgin ruwa kirar "Shandong", mai daukan jiragen yaki, har ma da bude babban filin jirgin sama na "Daxing" dake birnin Beijing da dai sauransu.

Game da bukin cika shekaru 70 da kafa kasar Sin, Lawal ya ce, shi dai ganau ne, domin ya ga fareti mai ban sha'awa, inda dubban 'yan kasar Sin suka fito da farin ciki domin kallon sojoji da kuma kayan yaki kirar kasar Sin, wadanda aka nuna a fili Tian'anmen, yana mai cewa abin da ya burge shi kwarai.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China