Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Nijeriya: Hadin kan Sin da Afrika abin koyi ne ga kasa da kasa
2020-01-03 10:32:50        cri

Jiya Alhamis, shugaban cibiyar nazarin kasar Sin dake Nijeriya Charles Onunaiju ya wallafa wani sharhi a jaridun Vanguard da The Sun, inda ya bayyana cewa, an cimma nasarori masu armashi a cikin shekaru 20 tun bayan kafuwar taron dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, kuma hadin kan bangarorin biyu ya zama wani sabon salon dangantakar kasa da kasa.

Bayanin ya ce, a cikin farkon shekaru 20 na karni na 21, Sin ta farka kuma ta samu bunkasuwa a fannoni dadan-daban. Dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da aka kafa a shekarar 2000 ya kafa makoma mai haske ga dangantakar kasa da kasa, matakin da ya shaida cewa, dangantakar abota ta hadin kai bisa ka'idoji biyar na yin zama tare cikin lumana ta fi kulla kawance mai kyau, kasashen dake da mabambanta tsare-tsaren zaman al'ummar kasa, da hanyoyin bunkasuwa za su iya kai ga matsaya daya ta hanyar yin tattaunawa da yin hadin gwiwa. Shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta samo asali daga kasar Sin, amma ta amfanawa duk fadin duniya. Wannan shawara ta samu amincewa daga kasashen Afrika, hadin kan Sin da Afrika ya bayyana boyayyen karfin Afrika wanda ya taimaka sosai. Duk da sauye-sauye da ake fuskanta a duniya, hadin kan Sin da Afrika zai ci gaba samar da makoma mai haske ga bunkasuwar Bil Adama. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China