Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karamin jakadan kasar Sin ya gana da gwamnan Lagos
2020-01-06 11:17:20        cri

Kwanan baya, karamin jakadan kasar Sin Chu Maoming ya gana da gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, inda suka yi musayar ra'ayi kan inganta hadin gwiwa a tsakanin sassa daban daban na kasashen 2.

A yayin ganawar, Chu Maoming ya ce, a matsayinta na rukuni mafi ci gaban tattalin arziki a Afirka da kasa mafi yawan mutane, Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwar Sin da Afirka. A shekarun baya, kasashen 2 sun yi amfani da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yin hadin gwiwar moriyar juna da samun ci gaba tare. Chu Maoming ya taya Sanwo-Olu murnar samun nasarar ziyartar kasar Sin, tare da nuna cewa, hukumomin kasashen 2 sun taka muhimmiyar rawa wajen kara azama kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen da kyautata dankon zumunci a tsakaninsu.Karamin ofishin jakadanci na kasar Sin da ke Lagos zai ci gaba da goyon bayan inganta mu'amalar da ke tsakanin hukumomin kasashen 2, da kafa huldar abota a tsakanin karin larduna da jihohi, a kokarin bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin kananan hukumomin kasashen 2.

A nasa bangare, malam Sanwo-Olu ya ce, jihar ta Lagos za ta yi koyi da kyawawan fasahohin kasar Sin, za ta fitar da karin manufofin ba da fifiko don kara zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da Sin a fannoni daban daban. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China