Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malami a Jami'ar Abuja: Tsokaci kan jawabin Shugaba Xi Jinping na sabuwar shekarar 2020
2020-01-01 16:36:22        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta 2020, a jiya, 31 ga watan Disamban 2019. Inda shugaba Xi ya yi bitar nasarorin da Sin ta samu cikin shekarar 2019, tare da fatan samun karin ci gaba a shekarar 2020.

Bayan gabatar da jawabin, Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, malami a tsangayar kimiyyar siyasa ta Jami'ar Abuja, ya aikowa sashen Hausa na CRI sakon Email, inda ya ce, akwai wasu abubuwa da suka dauki hankalinsa daga cikin bayanan shugaba Xi.

Na farko dai, Sinawa mutane ne masu aiki tukuru wajen samun ci gaban kai da kai, ba tare da jiran wata kasa ko wasu mutane sun kawo musu dauki ba, wanda ya yi dai dai da abun da shugaban ya fada cikin jawabin.

Na biyu kuma, akwai wata nasara da har kasashen da suka ci gaba akasarinsu ba su samu ba, amma a yau kasar Sin ta samu. Wannan nasara ta kasu gida uku kamar yarda shugaban ya lissafa, wato shawo kan manyan hadarurrun da za su iya kunno kai, da tallafawa matalauta, da magance matsalar gurbatar yanayi. Wadannan abubuwa, kasar Sin ce kadai ta iya samun ci gaba a kansu, a wannan lokacin da duniya ke ciki a yanzu.

Ban da wannan kuma, wani babban al'amari da ya ja hankalin Dr. Sheriff shi ne, fadin shugaban cewa "An kammala ayyukan kwaskwarima ga hukumomin jam'iyyar Kwaminis gami da na gwamnatin kasar Sin.". inda ya ce yaki da cin hanci da rashawa, abu ne da kasar ta tabbatar da shi kafin ta samu ci gaba. Yayin da kasar Sin take karfafa yaki a kan wannan, an samu raguwar wawure arzikin kasa ko almundahana, wanda lamari ne a ya samo asali daga garambawul da ake yi wa mambobin jam'iyyar kwaminis ta kasar. Yana mai bayyana shi a matsayin babban darasi ga kasashen Afirika.

A ganin Dr. Sheriff, ya kamata kasashen duniya su yi koyi da kasar Sin wajen kishin kasa. Dabi'ar kishin kasa abu ne da ya ja hankulan jama'a musamman wajen bikin cika shekaru 70 da kafuwar kasar. Kuma Wakokin kishin kasa musamman wakar nan mai taken "Ni da kasarmu," ta kara hada kan 'yan kasar da kara musu kishi. Wannan ya zama abin koyi ga sauran kasashen duniya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China