Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 5 sun rasu sakamakon fashewar iskar gas a arewacin Nijeriya
2020-01-05 16:18:10        cri
Jiya Asabar, mutane 5 sun rasu, yayin da mutane 4 suka jikkata, sakamakon fashewar iskar gas da ta auku a jihar Kaduna.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa, da yammacin ranar 4 ga wata, wata tashar iskar gas dake garin Sabon Tasha na birnin Kaduna ta fashe ba zato ba tsammani, hadarin da ya haddasa rasuwar mutane 5, yayin da mutane 4 suka ji rauni. Kuma an riga an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Malam Yakubu ya kara da cewa, rundunar 'yan sanda ta fara gudanar da bincike kan dalilin aukuwar hadarin.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya fidda wata sanarwa, inda ya nuna juyayi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China