Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattijan Nijeriya
2020-01-06 10:37:12        cri
A kwanakin baya, jakadan Sin dake tarayyar Nijeriya Zhou Pingjian, ya gana da shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattijan kasar Sanata Adamu Bulkachuwa.

Yayin zantawar su, Zhou Pingjian ya bayyana cewa, Sin da Nijeriya kawayen juna ne bisa manyan tsare-tsare, wadanda suka nuna goyon baya ga juna kan manya batutuwan dake shafar moriyarsu. Ya ce shekarar bana shekara ce a ta cika shekaru 20 da kafa dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Ya ce Sin tana son yin kokari tare da Nijeriya, wajen aiwatar da ayyukan da aka tsara a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa, da raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da kuma zurfada hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakaninsu a dukkan fannoni.

A nasa bangare, sanata Bulkachuwa, ya yabawa kasar Sin bisa babban ci gaba da ta cimma a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, yana mai cewa, Sin ta taimakawa kasashe masu tasowa wajen daidaita matsaloli da dama, kuma hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya a dukkan fannoni, ya haifar da moriya ga jama'ar kasar Nijeriya.

Sanatan ya ce ya taba ziyartar yankin Xinjiang, inda ya ga bunkasuwar yankin, da yanayin aiwatar da manufofin addinai da kabilu na Sin a yankin. Ya ce wasu kasashe na zargi kasar Sin ba tare da dalili ba, suna kuma yunkurin tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, to sai dai a cewar sa, za su ci tura. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China