Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An raunata jami'an kiyaye zaman lafiyar MDD 18 a harin Mali
2020-01-10 10:31:56        cri

Kimanin jami'an shirin wanzar da zaman lafiya na MDD da suka fito daga kasar Chadi 18 ne aka raunata a harin da aka kaddamar a sansanin sojoji dake arewacin kasar Mali, kakakin MDD ne ya bayyana hakan.

Stephane Dujarric, kakakin MDD ya bayyana cewa, ofishin shirin kiyaye zaman lafiyar na MDD dake Mali ya ba da rahoton cewa, an harba wasu rokoki a sansanin sojojin dake Tessalit a yankin Kidal, inda dakarun kiyaye zaman lafiyar MDDr suke zama ne tare da sojojin Mali da sojojin kasa da kasa.

Dujarric ya kara da cewa, rahotannin farko sun nuna cewa, an jikkata dakarun MDD 18 da suka fito daga kasar Chadi, daga cikinsu akwai wasu 6 da suka samu munanan raunuka.

Kasar Mali tana fuskantar rikicin siyasa da tabarbarewar al'amurran tsaro da kuma fadan kabilanci tun daga watan Maris na shekarar 2012. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China