Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a kasar Mali
2019-10-10 16:19:28        cri
Kwamitin sulhun MDD ya bukaci bangarorin da abin ya shafa a kasar Mali da su ingiza matakan aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wadda aka cimma matsaya kanta a shekarar 2015.

Kwamitin MDDr ya lura cewa an dan samu cigaba game da batun aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar tsakanin gwamnatin Mali da kungiyoyin masu dauke da makamai dake arewacin kasar.

Haka zalika kwamitin sulhun MDDr ya yi maraba da kaddamar da shirin shigar da dukkan bangarorin kasar cikin shirin tattaunawar sulhun kasar wanda ya kunshi kafa wasu matakai da dake shafar yadda za'a kammala yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar. An shawarci dukkan masu ruwa da tsaki a kasar da su shiga taron tattaunawar sulhun domin samun nasarar cimma matsaya game da zaman lafiyar kasar. (Ahmad Gagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China