Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe sojan Faransa a Mali
2019-11-03 16:06:41        cri
An hallaka wani sojan Faransa a kasar Mali bayan da wata tankar yakin da yake ciki ta taka wasu abubuwan fashewa, wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ta tabbar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Corporal Ronan Pointeau, yana aiki da runduna ta farko ta sojojin Faransa dake Valencia, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake tsaka da gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya inda motar da yake tukawa ta taka wasu abubuwan fashewa da aka binne, in ji sanarwar.

Macron ya jinjinawa dakarun sojojin da suka sadaukar da kansu kana ya bayyana cikakken goyon bayansa da nuna kwarin gwiwa ga sojojin Faransa da dakarun kawance a kokarin ta suke wajen yaki da ta'addanci.

Shugaba Macron ya kara da cewa, ya kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel.

A watan Janairun 2013, Faransa ta kaddamar da mummunan harin soji da nufin fatattakar mayakan 'yan tada kayar baya wadanda suka yi barazanar karbe ikon birnin Bamako, helkwatar kasar Mali. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China