2019-10-09 09:34:10 cri |
Wu Haitao, ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar cewa, ya kamata dukkan bangarorin kasar Mali su yi amfani da damar da babban taron ya samar, su hada hannu don samun zaman lafiya da ci gaba a kasar, tare da warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa.
Ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su bada gudunmuwa mai ma'ana ga kasar Mali, tare da taimakawa wajen karfafa tsarin shugabanci da na ci gaban kasar.
Har ila yau, wakilin na kasar Sin ya ce, kamata ya yi takunkumin kwamitin sulhu a kasar, ya tabbatar da kiyaye manufofin da kwamitin ya gabatar, tare da taimakawa wajen kyautata tsarin siyasar kasar.
Ya kuma yi kira ga kasashen duniya su taimaka wajen bunkasa harkokin tsaron kasar ta yadda gwamnati za ta iya daukar nauyin tabbatar da tsaron kasar da kanta. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China