Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta ayyana jagoran kungiyar 'yan tada kayar bayan Mali a matsayin dan ta'adda
2019-11-08 11:31:16        cri

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana Amadou Kouffa, babban jami'in kungiyar 'yan tada kayar bayan yammacin Afrika a matsayin dan ta'adda na kasa da kasa (SDGT).

A wata sanarwar da ma'aikatar harkokokin wajen Amurkar ta fitar ta ce, Kouffa, babban mamban kungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), shi ne ya jagoranci kaddamar da hari kan dakarun sojojin kasar Mali a farkon wannan shekarar, wanda ya yi sanadiyyar kashe sojoji sama da guda 20.

Dukkan dukiyar da ya mallaka wanda ke karkashin kulawar Amurka za'a rike su, kuma hukumomin Amurka sun haramta yin duk wata hulda da shi.

A cewar sanarwar, JNIM kungiya ce dake da dangantaka da al-Qaida wacce take da karfi a yankin Sahel na Afrika. Kungiyar ta'addancin ta sha daukar nauyin kaddamar da wasu hare hare da yin garkuwa da mutane tun daga watan Maris na shekarar 2017, kana ta hallaka fararen hula sama da 500.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China