Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Mali 5 sun mutu sakamakon wani hari
2020-01-07 09:31:04        cri

Rundunar sojin Mali ta sanar a jiya Litinin cewa, sojoji 5 sun mutu sakamakon harin bom da aka kai yankin Ségou dake tsakiyar kasar.

Sanarwar ta ce, ayarin motocin rundunar sojin Mali ta gamu da harin bom ne yayin da ya ke aikin rakiyar wasu motoci a wannan yanki da sanyin safiyar Litinin, lamarin da ya yi sanaddiyar mutuwar sojoji 5, yayin da wasu 4 suka ji rauni da kuma lalata motoci 4.

An ba da labarin cewa, watan Maris na shekarar 2012, aka yi juyin mulki a kasar Mali, a cikin watan Afrilun shekarar 2013 kuma, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin kafa shirin wanzar da zaman lafiya na MINUSMA a kasar. Sannan, a watan Mayun shekarar 2015 ne, gwamnatin Mali da wasu rundunoni dake arewacin kasar, suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu, kuma a watan Yuni na wannan shekara, bangarorin daban-daban da abin ya shafa suka kulla yarjejeniyar. Duk da hakan, an rika samun rikice-rikice a arewacin Mali a shekarun baya-baya, har ma da yankin tsakiyar kasar, inda yake fama da karin hare-hare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China