Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta buga karin haraji kan wasu kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka ba
2019-12-15 16:07:45        cri

Kwamiti mai kula da tsarin haraji na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya yanke shawara cewa, Sin ba za ta buga karin haraji kan wasu kayayyakin da za a shigo da su daga Amurka na kashi 10 cikin dari da na kashi 5 cikin dari ba, wanda aka shirya bugawa daga karfe 12 na ranar 15 ga wata, bisa dokar harajin kwastam ta jamhuriyyar jama'ar kasar Sin da dokar cinikayyar shigi da fice ta jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, don tabbatar da sakamakon da aka samu cikin shawarwarin kasashen biyu kan tattalin arziki da cinikayya. Matakin da ya sa Sin ta dakatar da buga karin haraji kan motoci da kayayyakin gyara na motocin da za ta shigo da su daga Amurka. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da matakan buga karin haraji kan sauran kayayyaki kirar Amurka yadda ya kamata, da kuma kara takaita takardar sunayen kayayyakin buga haraji.

Sin tana fatan cewa, ita da Amurka za su ci gaban da yin hadin gwiwarsu da bin hanya iri daya don daidaita batutuwan dake jawo hankalinsu da ingiza bunkasuwar dangantakar tattalin arziki da ciniki tsakaninsu yadda ya kamata bisa adaci da mutunta juna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China