Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta mai da martani kan dokar tsaro na shekarar 2020 na Amurka dake shafar kasar Sin
2019-12-21 19:57:00        cri

Mai magana da yawun kwamiti mai kula da harkokin ketare na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin You Wenze ya mai da martani kan dokar danka izni game da tsaron kasar Amurka na shekarar 2020, wadda Amurka ta yi shirin zartas da ita, inda ya bayyana cewa, Amurka ta yi biris da rashin jin dadi sau da dama da Sin take bayyana kan wannan batu, har ta shigar da wasu ayoyi maras kyau dake shafar yankin Taiwan, Hong Kong da Xinjiang da dai sauransu, abin danne gaskiya ne da nuna bambancin ra'ayi, kuma matakin tamkar shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.

You Wenze ya ce, Sin na kalubalantar Amurka da ta yi watsi da tunanin cacar baka da babakere, da daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da kuma daukar matakan da suka dace don kawar da illa da ta haifar, don kiyaye dangantakar Sin da Amurka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China