Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar harajin Sin ta gabatar da jerin hajojin Amurka da ba za ta kara musu haraji ba
2019-12-19 15:04:55        cri
Yau Alhamis, hukumar haraji ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta sanar da "jerin hajojin Amurka da Sin ba za ta kara musu hajoji ba", wannan shi ne jerin sunaye na biyu da majalisar gudanarwar kasar Sin ta zartas kan hajojin Amurka da Sin ba za ta kara musu haraji ba, kana karo na biyu na jerin hajojin Amurka da Sin ta tsame daga kara musu haraji, wanda kasar ta fidda karo na farko.

Daga ranar 26 ga wata Disamba na shekarar 2019 zuwa 25 ga watan Disamba na shekarar 2020, kasar Sin ba za ta karbi karin haraji kan wadannan hajojin kasar Amurka ba, domin mai da martani kan dokar harajin Amurka mai lamba 301 da ta fidda. Sai dai kuma, kasar Sin ba za ta mayarwa Amurka kudaden harajin da ta karba kan hajojinta na baya ba. Amma game da sauran hajojin da Sin ba ta cire daga jerin wadanda za a kara musu haraji ba, za ta ci gaba da karban karin haraji.

A nan gaba kuma, hukumar za ta ci gaba da cire wasu hajoji daga jerin wadanda za a kara musu harajin, sa'an nan, za ta fitar da sanarwa game hajojin da aka tsame daga jerin wadanda za a kara buga musu haraji a lokacin da ya dace. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China