Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka na kara tuntubar juna kan ragowar ayyuka bayan sun tabbatar da abubuwan dake cikin yarjejeniyar da za su kulla
2019-12-19 20:03:03        cri

Kwanan baya, Sin da Amurka sun kai ga cimma matsaya daya, kan abubuwan dake cikin yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a mataki na farko.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Gao Feng, ya zanta da manema labarai a yau Alhamis a nan birnin Beijing, inda ya nuna cewa, tawagogi masu kula da harkar tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu, na kara tuntubar juna da yin musanyar ra'ayi, kan yadda za a kulla wannan yarjejeniya, da dai ragowar ayyuka masu nasaba da ita. Za kuma a gabatar da hakikanin abu dake cikin yarjejeniyar, a lokacin da suka sa hannu kan ita.

Bisa sanarwar da Sin ta fitar, an ce Amurka za ta cika alkwarinta na kawar da karin harajin kwastam da ta bugawa kasar Sin bisa mataki mataki, da kuma tabbatar da rage karin harajin kwastam da za ta bugawa kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China