Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hada siyasa da kudi ya shaida ainihin ma'anar demokuradiyyar Amurka
2019-12-26 13:04:33        cri
Kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta gabatar da wani bayani mai taken "Hada siyasa da kudi ya shaida ainihin ma'anar demoradiyyar kasar Amurka", inda aka yi nuni da cewa, hada siyasa da kudi shi ne muhimmin dalilin da ya sa ake nuna kiyayya da juna a tsakanin bangarorin siyasa, da kuma tsakanin bangarorin zamantakewar al'ummar kasar Amurka.

"Kudi ya ciyar da siyasa" ya shaida hakikakin yanayin siyasa na kasar Amurka a halin yanzu. A fannin zabe, Amurka ta maida aikin zabe a matsayin zabe a tsakanin masu arziki. An yi nuni da cewa, tun daga karnin 21, yawan kudin da 'yan takara na jam'iyyu biyu na kasar suka kashe kan zabe ya karu daga dala miliyan 700 a shekarar 2004, zuwa dala biliyan 2 a shekarar 2012.

A shekarar 2016, yawan kudin da aka kashe kan dukkan zabukan kasar, ciki har da zaben shugaban kasar, da zaben majalisar dokokin kasar ya kai dala biliyan 6.6, wanda ya zama matsayin koli a tarihin kasar.

Kana an shigar da kudi da dama cikin sirri, cikin aikin zaben kasar Amurka. Bisa labarin da tashar internet ta kafar NBC ta kasar Amurka ta bayar a shekarar 2018, ma'aikatar kudi ta kasar ta sanar da cewa, ba za a bukaci yawancin kungiyoyin da ba na neman riba ba, su gabatar da yawan kudin da aka samar musu, hakan ya gaza gano wasu kudaden da aka yi amfani kan zabe.

A ganin bayanin, an kawo babbar illa ga kasar Amurka domin hada siyasa da kudi, an kwace hakkin siyasa na fararen hula, masu arziki da dattijai ne kawai ke mallaki mukamin siyasa, da samar da moriya ga masu arziki, don hakan an tsananta matsalolin siyasa da zamantakewar al'ummar kasar, kamar su matsalar bindiga da sauransu.

An yi nuni da cewa, an haifar da siyasar kudi domin tsarin jarin hujja. Bisa wannan tsari, an hada moriyar tattalin arziki da ikon siyasa, kuma 'yan takara na jam'iyyun biyu na kasar, su ne wakilan bangarori daban daban na jarin hujja.

An kuma jaddada cewa, hada siyasa da kudi ya shaida hakikakin yanayin zamantakewar al'ummar kasar Amurka. A cikin wannan yanayi, idan babu kudi, ba za a samu izinin tattaunawa kan harkokin siyasa ba, siyasar kudi ta zarce hakkin dan Adam mai salon kasar Amurka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China