Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
China na adawa da matakin majalisar wakilan Amurka na zartar da dokar Hong Kong
2019-10-16 11:10:42        cri
Kasar Sin ta bayyana tsananin fushi da adawa da matakin majalisar wakilan Amurka, na zartar da dokar kare hakkin dan Adam da Demokradiyya ta Hong Kong.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Geng Shuang, ya ce Majalisar wakilan Amurka tana sakaci da tauye gaskiya, bisa mayar da manyan laifukan kamar na cinna wuta da fasa shaguna da farwa 'yan sanda, matsayin batun kare hakkin dan Adam da demokradiyya, yana mai cewa wannan tsantsar rashin adalci ne.

Ya ce Kasar Sin za ta dauki matakai masu karfi na tunkarar matakan Amurka, da nufin kare cikakken 'yanci da muradunta na tsaro da na ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China