Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da littafi dangane da jawaban Xi Jinping na murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin
2020-01-06 11:18:00        cri

Kwanan baya, an kaddamar da wani littafi dangane da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi na murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar, a ciki da wajen kasar Sin, cikin harsunan Sinanci da Ingilishi.

Shekarar 2019, shekara ce ta cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Shugaba Xi Jinping ya halarci wasu manyan bukukuwa tare da gabatar da jabawai masu muhimmanci, wadanda suka jibanci tarihin jamhuriyar jama'ar kasar Sin cikin shekaru 70, inda jama'ar kasar suka yi gwagwarmaya ba tare da kasala ba, suka kuma hada kansu ba tare da baya ba, da kuma nuna aniyar raya kasa a sabon zamani. Jawaban Xi Jinping sun nuna babbar aniyar kasar Sin ta raya kasa cikin lumana da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, sun karfafa gwiwar al'ummar Sin ta kishin kasa, da sa kaimi kan 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da sojojin kasar da al'umomin kasar, kana sun inganta alfaharin da Sinawa 'yan kaka gida suka yi, sun jawo hankalin kasashen duniya sosai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China