Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi zai gabatar da jawabin sabuwar shekara
2019-12-30 19:29:33        cri

A gobe da misalin karfe 7 na almuru, bisa agogon Beijing ne ake sa ran shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gabatar da jawabin sa na sabuwar shekara.

Shugaban zai gabatar da jawabin da za a watsa ta kafofin yayata bayanai na rukunin CMG da kuma ta yanar gizo.

Kafofin da za su yada jawabin shugaban kai tsaye, sun hada da gidan talabijin na CCTV, da tashar "news channel", da tashar "Chinese international", da tashoshin dake watsa labarai da harsunan waje na CCTV, da China National Radio wato CNR, da gidan radion kasar Sin na CRI, sai kuma shafukan yanar gizo, da sabbin kafofin sada zumunta na manyan kafofin watsa labaru mallakar gwamnatin tsakiyar kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China