Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya sanya hannu kan kudurin horas da rundunonin soji
2020-01-02 19:56:56        cri

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanya hannu kan wani kuduri na horas da dakarun rundunonin sojin kasar, kudurin da ya kasance na farko, da hukumar gudanarwar rundunar sojin kasar ta amince da shi a bana.

Shugaba Xi wanda kuma shi ne babban sakataren hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar ta Sin, ya gabatar da kudurin, wanda zai samar da ikon karfafa ayyukan horas da dakarun sojin kasar a yanayi irin na yaki a zahiri. Kaza lika kudurin ya umarci rundunonin kasar, da su kasance cikin shirin ko ta kwana, da horo na shirin dauki ba dadi.

Har ila yau, kudurin zai kuma karfafa damar rundunar na gudanar da atisayen hadin gwiwa, da hade sabbin rundunoni cikin ayyukan gudanarwar dakarun sojin kasar.

Za a kara bunkasa horo tsakanin dakaru daban daban, da gwada karfin gudanarwar rundunar, da inganta karfin ta yadda ya kamata, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin wannan kuduri. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China