Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmancin aikin tantance kudaden ayyuka
2020-01-02 20:20:40        cri

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, ya ja hankalin sashen tantance kudaden gudanar da ayyuka na kasar, da ya kara azama wajen kara inganta ayyukan sa.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar ta Sin, kuma jagoran kwamitin koli na ayyukan tantance kudaden gudanar da harkokin hukuma, ya yi wannan tsokaci ne cikin wani umarni, bayan da a baya bayan nan, mahukuntan kasar suka jinjinawa ayyukan sashen tantance kudaden gudanarwa na gwamnati, da na daidaikun al'ummar kasar.

Shugaba Xi ya ce, sashen tantance kudaden gudanar da ayyuka, na taka muhimmiyar rawa, wajen aiwatar da manufofi da kwamitin kolin JKS ya amince da su, yana kuma tallafawa yakin da kasar ta Sin ke yi, da manyan kalubale uku, wato tabbatar da managarcin tsarin kashe kudade da raya tsarin tattalin arziki, da kyautata rayuwar al'umma, da kuma gina jam'iyya da gwamnati mai inganci.

Daga nan sai Xi ya bukaci hukumomin tantance kudaden gudanar da ayyukan da su ci gaba da ayyukan su yadda ya kamata, da martaba dokoki yayin aiki, da inganta dabarun aiki, ta yadda za su ba da babbar gudummawa ga aikin zamanantar da ginin kasa, da bunkasa ikon gwamnati na yin aiki yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China