Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jawabin Xi Jinping ya samu amincewa a kasashen ketare
2020-01-02 13:44:38        cri

A dab da zuwan sabuwar shekara, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabi na murnar sabuwar shekara ta 2020, jawabin da a kwanan nan ya samu yabo daga al'ummar kasa da kasa, inda suka jinjina yadda jama'ar Sin suka ci gajiyar ci gaban kasarsu, kana kasar Sin za ta tsaya kan kiyaye zaman lafiya a duniya da kara azama na samun bunkasuwa tare.

Kenneth Quinn, shugaban asusun kula da harkokin lambar yabo ta abinci na duniya ya ce, tanade-tanaden da suka shafi yadda kasar Sin ta raya kasa ta hanya mai inganci da kuma yaki da talauci a cikin jawabin Xi Jinping sun burge shi sosai. Raguwar yawan matalauta a kasar Sin, wata gaggarumar nasara ce da kasar Sin ta samu sakamakon sauya hanyar bunkasa tattalin arziki. Eric Mangonyi, wani masani daga jami'ar Walter Sisulu ta kasar Afirka ta kudu ya yi bayanin cewa, jawabin Xi Jinping na murnar sabuwar shekara yana da ma'ana, tamkar wani alkawari ne da ya yi wa jama'ar kasarsa, da ma jama'ar kasashen duniya baki daya. Jawabinsa ya nuna mana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da hada kai da kasa da kasa, a kokarin samun ci gaba tare ta hanyar aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Haka zalika, Robert Lawrence Kuhn, shugaban asusun Kuhn kuma masani ilmin harkokin kasar Sin a kasar Amurka ya ce, a cikin jawabin Xi Jinping, ya ambato cewa, duk da dimbin ayyukan da ya ke fama da shi, ya kan ware lokutan tattaunawa da jama'arsa, lamarin da ya burge mista Kuhn sosai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China