Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmancin layin dogo da aka kammala yayin da ake tunkarar gasar wasannin Olympics ta 2022
2019-12-30 21:14:12        cri

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin layin dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya da aka bude, wanda ya hada biranen Beijing da Zhangjiakou, a matsayin muhimmin aiki, a shirin kasarsa na karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu a shekarar 2022.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar ta Sin, ya yi wannan tsokaci ne a Litinin din nan, yayin bikin bude layin dogon da ya hada biranen biyu, wadanda za su karbi bakuncin gasar ta Olympics dake tafe. Ya kuma yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, da su tabbatar da kammalar sauran ayyuka masu nagarta.

An fara aikin ginin layin dogon na Beijing zuwa Zhangjiakou ne a watan Disambar shekarar 2015, a matsayin daya daga manyan ayyukan ababen more rayuwa da ake bukata, wajen cimma nasarar karbar bakuncin gasar ta Olympics dake tafe.

Bayan kaddamar da layin dogon, tafiya ta jiragen kasa masu saurin tafiya a kan sa, tsakanin birnin Beijing zuwa sassan gudanar da wasannin kankara na Zhangjiakou ba za ta kai sa'a guda ba.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China