Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jawabin Shugaba Xi Jinping Na Murnar Shiga Sabuwar Shekara Ta 2020
2019-12-31 19:34:27        cri

'Yan uwa da abokai, maza da mata:

Yayin da ake dab da shiga sabuwar shekara ta 2020, ina muku barka da sabuwar shekara da fatan alheri daga Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A shekara ta 2019, al'ummar kasar Sin sun himmatu wajen gudanar da ayyukansu kuma sun cimma nasarori masu dimbin yawa. Kasar Sin ta samu bunkasuwa mai inganci, har ma yawan GDPn kasar ya tasam ma Yuan triliyan dari, kuma matsakaicin yawan GDPn na kowane dan kasa ya kai dala dubu goma. Kasar Sin ta samu babban ci gaba a wasu muhimman ayyuka uku, ciki har da shawo kan manyan hadarurrukan da za su iya kunno kai, da tallafawa matalauta tare kuma da magance matsalar gurbatar yanayi. Bugu da kari, biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei na bunkasuwa tare yadda ya kamata, kuma yankin tattalin arziki dake kusa da kogin Yangtze da babban yankin Guangdong da Hong Kong da kuma Macao gami da yankin delta na kogin Yangtze na samun ci gaba cikin sauri. Haka kuma kasar Sin ta mayar da aikin kiyaye muhallin halittu dake kewaye da Rawayen kogi a matsayin manufar kasar. A shekarar ta 2019 kuma, gaba daya akwai kimanin gundumomi 340 a fadin kasar wadanda suka fita daga kangin talauci, inda mutane sama da miliyan 10 suka samu wadata. Na'urar binciken duniyar wata mai suna Chang'e-4 ta sauka a bayan duniyar wata mai nisa, al'amarin da ya zama karon farko a cikin tarihin dan Adam, sannan an yi nasarar harba roka Long March-5 mai dauke da kayayyaki, a waje daya kuma jirgin ruwan binciken kimiyya da fasaha mai suna Xue Long-2 ya je nahiyar Antatika, kuma tsarin shawagin tauraron dan Adam na Beidou ya shiga wani muhimmin lokaci, har ma an gaggauta samar da hidimar fasahar sadarwar 5G, an kuma fara amfani da babban filin jiragen sama na Daxing dake birnin Beijing. Namijin kokari gami da kwazon da al'ummar kasar Sin su ne suka sa kasar ta iya samun irin wadannan nasarori, wadanda ke shaida kwarjini da karfin da kasar ke da su.

A shekara ta 2019, manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofar ga kasashen waje da kasar take aiwatarwa ta kara samun ci gaba. An kammala ayyukan yin kwaskwarima ga hukumomin jam'iyyar Kwaminis gami da na gwamnatin kasar Sin. An kara kafa wasu sabbin yankunan gudanar da cinikayya cikin 'yanci na gwaji gami da sabuwar harabar yankin cinikayya maras shinge na gwaji a birnin Shanghai. An kuma fara kaddamar da wani nau'in takardar hannun jari a fannin yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a kasar Sin, kuma jimillar harajin da aka rage a kasar ya zarce Yuan triliyan 2. An kuma kara yawan albashin da za a rika cire haraji da kowane dan kasa zai biya, haka kuma, an rage farashin dinbin magungunan yau da kullum. Bugu da kari, Sinawa na iya amfani da kafar Intanet mai saurin gaske ba tare da kashe kudi da yawa ba, kuma gwamnatin kasar Sin ta yi kira ga jama'a su raba ire-iren shararsu na yau da kullum. Ana iya ganin manyan sauye-sauye da sabbin ci gaba a duk fadin kasar.

A shekara ta 2019 kuma, an ci gaba da yi wa harkokin tsaron kasa gami da rundunonin sojan kasar gyaran fuska, kuma rundunar sojan jama'ar kasar na kara samun karfi a sabon zamanin da muke ciki. Kasar Sin ta yi gagarumin bikin faretin soja, da gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kafa rundunonin sojojin ruwan teku da na sama, da gudanar da taron wasannin motsa jiki na sojojin kasa da kasa karo na 7. A wannan shekara kuma, an mika babban jirgin ruwan dakon jiragen saman yaki na farko da kasar Sin ta kera ga rundunar sojan tekun kasar. Hakika sojojinmu dake zama babbar ganuwar tsaro, suna matukar kokari wajen kare kasarmu, wadanda ya kamata mu jinjina musu!

A shekara ta 2019, wani babban al'amarin da ya fi burgewa shi ne murnar cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, inda muka jinjina wa dimbin nasarori da babban ci gaban da kasar ta samu a shekaru 70 da suka shige. A yayin bikin, sojoji masu karfin gaske sun yi maci a babban filin Tian'anmen, inda jama'a suka yi jerin gwano domin bayyana farin-cikinsu, yayin da aka yi ta rera wata wakar Sinanci dake nuna kishin kasa mai suna "Ni da kasarmu" ta samu karbuwa a kowane lungu. Ra'ayin kishin kasa ya kara karfafa hadin-gwiwar al'ummomin kasar Sin, har ma ya kara ba mu karfi wajen raya kasa.

A shekara ta 2019, ni da kaina na yi tattaki zuwa wurare daban-daban na kasar. An fara gina sabon yankin Xiong'an, kuma mashigin tekun Tianjin ya samu ci gaba cikin sauri, yayin da sabuwar cibiyar birnin Beijing ke bunkasa cikin sauri. Har wa yau, babban filin ciyayi na jihar Mongoliya ta gida na da kyan-gani, Rawayen kogi na da fadi, zirin da ya ratsa lardin Gansu ya samu bunkasa, haka kuma yankunan dake kewaye da kogin Hungpu na samun arziki da zaman wadata. A takaice, ana iya ganin bunkasuwa da zaman wadata a sassa daban-daban na kasar Sin. Na kuma sake ziyartar wasu muhimman wuraren kasar wadanda suka taka muhimmiyar rawa a lokacin juyin-juya-halin kasar. Daga garin Yudu na lardin Jiangxi inda jajayen sojoji suka taru don fara yin doguwar tafiya zuwa dakin adana kayan tarihin juyin-juya-hali na yankin Soviet dake gundumar Xin ta lardin Henan, da lardunan Hubei da Henan da Anhui suke kewaye da shi, sannan daga babban dutsen tunawa da jajayen sojoji reshen yamma dake garin Gaotai na lardin Gansu zuwa wurin tunawa da lokacin juyin-juya-hali dake Xiangshan na birnin Beijing, duk wadannan wuraren tarihi sun sa na yi tunani mai zurfi. Burinmu tun farkon farawa da bai kamata mu manta da shi ba, da babban nauyin dake rataye a wuyanmu, su ne kuzarin da ya sa mu ci gaba da kokari a sabon zamanin da muke ciki.

Kamar yadda na yi a lokutan baya, duk da cewa ina fama da aiki, na yi kokarin samun lokacin kai ziyara a tsakanin al'umma, inda suka gaya mini abubuwan da suke cikin zukatansu, wanda ban taba mantawa ba. 'Yan kabilar Dulong dake yankin Gongshan na lardin Yunnan, da mazauna kauyen Xiadang dake gundumar Shouning ta lardin Fujian, da dukkan sojojin reshen Wangjie, da dalibai masu karatun digiri na biyu a jami'ar nazarin harkokin motsa jiki ta Beijing, da wasu yara da tsoffi masu aikin sa-kai a yankin Macao, duk sun rubuto mini wasiku, inda na jinjina musu saboda nasarorin da suka samu, da yi musu gaisuwa da fatan alheri.

Bugu da kari, a shekarar da ta shude, akwai mutane da al'amura da dama wadanda suka burge mu kwarai da gaske. Tsohon soja wanda ya tsaya ga aikin bautan kasa amma ba tare da gayawa wasu ba mai suna Zhang Fuqing, da wata jami'ar da ta sadaukar da kanta ga aikin tallafawa matalauta mai suna Huang Wenxiu, da wasu 'yan mazan jiya 31 wadanda suka sadaukar da rayukansu ga aikin kashe gobara a yankin Muli dake lardin Sichuan, da wani soja mai suna Du Fuguo wanda ya rasa dukkan hannaye da kafafunsa sakamakon kare abokan aikinsa daga fashewar bam, tare kuma da kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin wadda ta lashe dukkan gasanni 11 na cin kofin duniya ta kwallon raga. Duk wadannan mutane da suka yi namijin kokari ko sadaukar da kansu ga ayyukan gina kasa sun zama jarumai, wadanda ya kamata mu rika tunawa da su har abada.

A shekara ta 2019, kasar Sin ta ci gaba da bude kofarta ga duk duniya baki daya. Mun shirya babban dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu, da bikin baje-kolin lambunan shan iska na kasa da kasa a Beijing, da babban taro kan wayewar kai na nahiyar Asiya, da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu wato CIIE, inda muka shaidawa duniya wata kasar Sin mai wayewar kai da nuna hakuri da son bude kofarta ga kasashen waje. Ni da kaina na yi shawarwari tare da takwarorina na kasashe da dama, inda na bayyana musu manufofin kasar Sin, da kara dankon zumunci da zurfafa cimma ra'ayi iri daya. Har yau, an kara samun wasu kasashe wadanda suka kulla dangantakar jakadanci da kasar Sin, abun da ya sa adadin kasashen da suka kulla dangantakar diflomasiyya da kasar Sin ya kai 180. Yanzu kasar Sin tana da aminai a ko'ina a fadin duniya!

Sabuwar shekara ta 2020, shekara ce mai ma'ana ta musamman. Za mu cimma burinmu na raya zaman al'umma mai matsakaicin wadata, da samar da al'umma mai matsakaicin ci gaba ta kowace fuska ya zuwa lokacin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta yi bikin murnar cika shekaru dari da kafuwa a shekara ta 2021. Shekara ta 2020 muhimmiyar shekara ce gare mu wajen samun galaba kan yakin kawar da talauci a duk fadin kasar. Ya kamata mu zage damtse wajen ganin mun yi nasarar kawar da duk wata wahala da hadari, da kyautata ayyukanmu, da aza tubali mai inganci, don samun nasarar yaki da fatara, da cimma burin kawar da kangin talauci baki daya a yankunan karkara da gundumomi masu fama da talauci a karkashin mizanin da ake ciki a halin yanzu.

A kwanakin baya na halarci bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin Macao karkashin ikon babban yankin kasar Sin, inda na yi farin-cikin ganin bunkasuwa da zaman lafiya da kwanciyar hankali da yankin ya samu. Irin nasarorin da yankin Macao ya samu sun nuna cewa, an yi nasarar aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" yadda ya kamata wadda ke samun amincewa daga al'ummar yankin. A watannin da suka gabata, ana maida hankali sosai kan yanayin da ake ciki a Hong Kong. In babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, yaya za'a mu ji dadin rayuwa! Ina matukar fatan ganin bunkasuwar Hong Kong, inda jama'a za su iya jin dadin zaman rayuwa ba tare da matsala ba. Samun ci gaba da zaman karko shi ne burin al'ummar yankin Hong Kong, kuma shi ne babban fata na daukacin al'ummar kasar Sin.

Idan mun dubi baya, za mu ga cewa, mu ga yanayin na zaman lafiya, mun kuma ga tashe-tashen hankula. Amma babu yadda muka iya sai mu nuna jaruntaka don mu iya haye wahalhalun da muke fuskanta. Kasar Sin za ta nace ga bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, da shimfida zaman lafiya a duk duniya, da neman ci gaba tare. Muna fatan yin kokari kafada da kafada tare da al'ummun kasashen duniya, da himmatuwa wajen bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya", da raya kyakkyawar makomar al'umma ta bai daya, a wani mataki na samar da makoma mai haske ga daukacin al'umma.

A halin yanzu, akwai mutane da dama wadanda ke aiki tukuru da nuna kwazo da tabbatar da zaman lafiya. Ina jinjina muku!

Ina kira a gare mu baki daya, da mu kara kokari yayin da muke murnar shiga sabuwar shekara ta 2020.

Barka da sabuwar shekara!(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China