Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagoran kamfanin Boeing yi yi murabus
2019-12-24 13:42:32        cri
Kamfanin jiragen sama na Boeing na kasar Amurka ya fidda sanarwa a jiya Litinin cewa, jagoran kamfanin Dennis Muilenburg ya yi murabus. Kana, shugaban hukumar zartaswa na kamfanin Dave Calhoun ya maye gurbinsa.

Kafofin watsa labarai na kasar Amurka sun fidda labarai dake cewa, Dennis Muilenburg ya yi murabus ne, sakamakon hadarin faduwar jiragen saman kamfanin na Boeing masu samfurin 737MAX guda biyu, wadanda suka haddasa rasuwar mutane 346. Sa'an nan, an daina yin amfani da jirgin sama mai samfurin 737MAX a duk fadin duniya, aka kuma gudanar da bincike masu dimbin yawa kan wannan batu, lamarin da ya kawo illa ga dukkanin kamfanonin jiragen sama masu amfani da wannan samfurin jirgi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China