Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An saki Indiyawa 18 da 'yan feshin teku suka sace a gabar ruwan Najeriya
2019-12-23 20:49:57        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, an saki Indiyawa 18 da wasu 'yan fashin teku suka yi awon gaba da su a kusa da gabar ruwan Najeriya.

Rundunan sojojin ruwan Najeriya da wani kamfanin jigila ta ruwa sun tabbatar da sakin 'yan kasar Indiya guda 18 da aka yi awon gaba da su daga wani jirgin ruwa a ranar 3 ga watan Disamba.

Karamin ofishin jakadancin kasar Indiya dake Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya bayyana godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen sako 'yan kasar nata cikin koshin lafiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China