Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 25 sun mutu a sakamakon hadarin mota mai tsanani da ya faru a Nijeriya
2019-12-14 15:53:54        cri
'Yan sandan Nijeriya sun tabbatar a jiya cewa, an samu wani hadarin mota mai tsanani a jihar Bauchi dake arewo maso gabashin kasar a ranar 12 ga wannan wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 25, tare da raunatar mutum guda mai tsanani.

'Yan sandan jihar Bauchi sun gaya wa 'yan jarida cewa, a ranar 12 ga wannan wata, wata motar bas dake dauke fasinjoji 22 da wata mota dake dauke mutane 4 sun yi karo a kan hanyar mota dake jihar, daga baya motocin biyu sun kama wuta. Bayan da aka kai mutanen 26 zuwa asibiti, an tabbatar da mutuwar 25 daga cikinsu, kuma saura daya ya ji rauni mai tsanani, kuma ana ci gaba da kokarin ceto raguwar shi.

'Yan sandan sun fara bincike kan dalilin da ya haddasa wannan hadarin, kana sun yi kira ga jama'a da su guji tukin ganganci.

A sakamakon hanyoyin motoci marasa inganci, da daukan mutane fiye da kima, da kuma gudun fiye da kima, suna haifar da yawan hadarorin motoci a Nijeriya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China