Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya bayyana damuwa game da kashe fararen hula da yin garkuwa da wasu a Najeriya
2019-12-25 13:20:19        cri
Jami'in MDD ya bayyana damuwa game da kashe fararen hula da yin garkuwa da wasu a Najeriya

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa game da wasu rahotannin kashe fararen hula da yin garkuwa da wasu wadanda 'yan bindiga suka aiwatar a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin wata sanarwa, kakakin babban sakataren MDDr Stephane Dujarric ya ce, Guterres ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, kana ya bayyana cikakken goyon bayan MDD ga al'ummar Najeriya da gwamnatin kasar.

Sanarwar ta ruwaito babban sakataren yana cewa, hare-haren da 'yan bindigar ke kaddamarwa kan fararen hula, da jami'an aikin agaji, da lalata kayayyakin more rayuwar jama'a, ya sabawa dokokin kasa da kasa. Kuma tilas ne a hukunta wadanda ke daukar nauyin wadannan munanan ayyukan.

Dole a ba da cikakkiyar kariya ga dokar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa, da dokar ba da kariya ga ma'aikatan agaji ta kasa da kasa, kana dole ne a kare dukkan fararen hula a Najeriya, in ji sanarwar.

Rahotanni sun ce an kashe fararen hula masu yawan gaske kana an yi garkuwa da wasu a ranar Litinin da ta gabata a arewacin jahar Borno, da kan hanyar Damaturu zuwa Biu, wacce ta hada jahohin Borno da Yobe. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China