Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta kan dokar tsaro ta shekarar 2020 da Amurka ta sanyawa hannu
2019-12-23 20:35:37        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana rashin jin kasarsa game da matakin bangaren Amurka na baya-bayan kan dokar tsaro ta shekarar 2020 da ta sanya wa hannu, ayar dokar da ta kunshi jirkita da ma takalar yadda kasar Sin ke raya harkokinta na soja da bayanai da ba su dace ba kan yankunan Taiwan da Hong Kong da Xinjiang, da kuma haramta sayan wasu muhimman hajojin kasar Sin.

Rahotanni na cewa, ayar dokar da bangaren Amurka ya sanya wa hannu, ta kuma amince da kafa sansanin sojan samaniya a hukumance. Babban hafsa a rundunar sojojin saman Amurka ya bayyana cewa, kasashen Sin da Rasha babbar baraza ce ga Amurka, kana Amurka tana bukatar runduna mai karfi domin ta tunkari karfin kasashen Sin da Rasha a fannin sararin samaniya.

Dangane da wannan batu, Geng Shuang ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan, duk da adawa da kasashen duniya ke nunawa, Amurka tana kara karfinta na ganin ta jagoranci harkokin sararin samaniya, da ma kara fadada tasirinta a fannin mallakar makamai da mayar da sararin samaniya zama fagen daga.

Geng ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin tana yayata bukatar amfani da sararin samaniya cikin lumana, tana kuma adawa da mallakar makamai da ma tseren mallakar makamai a sararin samaniya. Kasar Sin tana fatan al'ummomin kasa da kasa, musamman masu karfin fada aji a duniya, za su rika nuna halin ya kamata, wajen ganin ba su mayar da sararin samaniya zama wani sabon fagen daga ba, da yin aiki tare don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sararin samaniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China