Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya yi kira ga dakarun PLA a Macao da su kara zage damtse wajen kyautata ayyukan su
2019-12-20 20:31:50        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga dakarun rundunar 'yantar da al'ummar kasar Sin ko PLA dake Macao, da su kara zage damtse wajen kyautata ayyukansu, su kuma ba da karin gudummawa wajen cimma nasarar aiwatar da manufar "Kasa daya, tsarin mulki biyu" a yankin na Macao.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS, kana shugaban kwamitin kula da harkokin soja na kwamitin tsakiyar kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne a Juma'ar nan, lokacin da yake duba rundunar ta PLA dake yankin Macao. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China