Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping da Donald Trump sun yi hira ta wayar tarho
2019-12-21 15:57:08        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hira da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a daren jiya Juma'a.

A cikin hirarsu, Trump ya nuna cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya daya kan yarjejeniyar tattalin arziki da ciniki a matakin farko, abin da ya amfanawa kasashen biyu har ma da duniya baki daya, hakan ya sa, kasuwannin kasashen biyu da na duniya suna maida martani mai yakini ga lamarin. Amurka tana fatan kara tuntubar kasar Sin don sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da jimawa ba, da kuma tabbatar da ita.

A nasa bangare, Xi Jinping ya ce, Sin tana sanya ido sosai game da kalamai marasa dadi da Amurka ke yi kan batun dake shafar yankunan Taiwan, Hong Kong, Xinjiang da Tibet da dai sauransu. Shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin take yi, hakan ba ma kawai yana illata muradun kasar Sin ba ne, har ma yana kawo cikas ga hadin kan kasashen biyu da amincewa da juna. Yana fatan Amurka ta tabbatar da matsaya wanda bangarorin biyu suka cimma a yayin ganawa sau da dama da suka yi, da kuma dora muhimmanci kan muradun kasar Sin, don kaucewar samun cikas cikin dangantakar kasashen biyu da wasu muhimman ajandojin da za su gudana.

Trump ya bayyana cewa, yana fatan kara tuntuba da yin mu'amala da kasar Sin ta hanyoyi daban-daban. Ya yi imani cewa, kasashen biyu za su daidaita bambancin ra'ayinsu yadda ya kamata da samun bunkasuwar dangantaka tsakaninsu cikin lumana. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China