Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Koriya ta Kudu
2019-12-23 16:13:45        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaran aikinsa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in a yau, a dakin taron jama'a dake birnin Beijing, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, a halin yanzu, ana fuskantar ra'ayin ba da kariya, da ra'ayin bangare daya, da ra'ayin kama karya a duniya, wadanda suka kawo illa ga sarrafa harkokin duniya da zaman lafiyar duniya.

Ya ce a matsayin kasa mai sauke nauyi dake wuyanta, kasar Sin ta kiyaye sa kaimi ga bunkasar duniya ta hanyar samun ci gaban kanta, tana kuma son kiyaye adalci da samun moriyar juna, da more dama, da daukar nauyi tare da kasa da kasa, don raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama.

Shugaba Xi Jinping, ya kuma yi maraba da shugaba Moon Jae-in, da ya halarci taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 8 a kasar Sin, yana mai nuni da cewa, a halin yanzu, kamata ya yi kasashen biyu su nuna kulawa ga moriyar juna, don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, shugaba Moon Jae-in ya yi nuni da cewa, a ganin kasarsa wato Koriya ta Kudu, harkokin yankin Hong Kong da na yankin Xinjiang, dukkansu su harkoki ne na cikin gida na kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China